TARIHIN IBRAHIM M. GOMBE

Date: 27-03-2017 8:31 am (7 years ago) | Author: Ibrahim M Gombe
- at 27-03-2017 08:31 AM (7 years ago)
(m)
Ni Mohammad Ibrahim wanda akafi sani da Ibrahim M. Gombe an haifeni ranar 01/01/1995 a kauyen Jauro-jatau dake gundumar Garko a karamar hukumar Akko dake jihar Gombe.
     A gidan mu ba abinda akafara nuna mana daga farko sai karatun Allo. Nayi karatun Al-Qur'ani agurin Mallam Salisu Isma'il dake kauyen Wuro Biriji daga 2001 zuwa 2006.
     Afannin karatun boko kuwa wato ta inda nafi karfi, nasoma karatun furamare a Wuro Biriji Primary School a shekara ta 2002 inda nakammala wato narubuta jarrabawar 'common entrance' a 2008 kuma na kasance nine 'class rep' har nagama.  A 2009 nashiga GDJSS Wuro Biriji inda nahada ashekarata 2011 kuma na kasance nine 'health prefect'. Akarshen 2011 nasamu 'scholarship' a makarantar 'Science Village Secondary School Gombe' a 2014 na rubuta jarrabawar SSCE {WAEC da NECO} da kuma JAMB. Nakasance nine 'headboy' namakarantar.
    A 2015 ne nashiga kwallejin horas da malamai takasa dake garin Gombe wato FCE(T)Gombe. Ina karantan Biology/Chemistry.
   A sana' kuma ni marubucine. 

Posted: at 27-03-2017 08:31 AM (7 years ago) | Newbie