CAN U UNDERSTAND THIS LANG

Date: 30-03-2010 9:57 pm (14 years ago) | Author: ABU ANISA
- at 30-03-2010 09:57 PM (14 years ago)
(m)
Wadansu matasa hudu sun shiga komar ’yansanda, inda ake zargin su da satar yara. Matasan, Abubakar Salisu (dan shekara 23) da Uzairu Aminu Kurfi (dan shekara 19) da Mohammed Sani Bello (dan shekara 21) da kuma Naziru Bala Sulaiman (dan shekara 19), ’yansandan da ke sintiri ne suka samu nasarar cafke su, a daren ranar Litinin da ta gabata, a yayin da suke kokarin sace wasu yara biyu, a kan titin Beirut da ke birinin Kano.

Kwamishinan ’yansanda na Jihar Kano, Mohammed J. Gana, ya shaida wa Aminiya cewa, lokacin da jami’ansa suka tsare motar matasan, sun gano wani yaro dan shekara takwas a cikin but din motar tasu. Ya kara da cewa, jami’an nasa sun samu wannan nasara ne a lokacin da suke yin sintiri a titin Beirut, inda suka samu wani yaro dan shekara 12 yana gudu, wanda ya gaya musu cewa, wasu masu satar yara ne suke bin shi, da nufin sace shi. Yaron ya shaida wa jami’an cewa, barayin yaran da ke neman sace shi, sun yi nasarar sace dan uwansa, mai suna Hassan Musa kuma sun garkama shi cikin but din motarsu.
Kwamishinan ’yansandan na Jihar Kano ya ce, lokacin da jami’ansa suka samu wannan bayani daga yaron da ya tsira, sai suka baza komarsu, inda suka yi nasarar tsare motar wadanda ake zargin, wacce kirar Honda ce mai lamba ‘Kano AY471 DAL,’ suka yi nasarar kama shugabansu mai suna Abubakar Salisu, wanda shi ne yaron ya yi zargin ya kama shi da karfi ya saka shi a but din motarsu. Kwamishinan ya kara da cewa, sauran matasan uku da suka tsere, jami’an sun yi nasarar kamo su ne a gidajensu da ke cikin birnin Kano.
Rundunar ’yansanda ta Jihar Kano, ta sha alwashin baza komarta da nufin bincikowa da kamo mutanen da ke daukar nauyin satar mutane a cikin birnin Kano. “Akwai wasu mutane da ke aiken su domin su sato musu mutane da nufin yin tsafi da su. Za mu mika wadannan matasa da ake zargi zuwa sashin binciken laifuffuka domin ci gaba da bincike. Muna son bin diddigin wannan al’amari, domin gano cewa shin barayin yaran nan suna zaune a nan Kano ne ko kuwa suna wani wuri ne daban? Mun san cewa suna da yawa, amma za mu samu cikakkun bayanai nan ba da jimawa ba, idan mun kammala bincikenmu.” Inji Kwamishina Mohammed J. Gana.
Da yake kira ga al’umma, Kwamishinan ya gargadi iyayen yara da su daina tura yaransu zuwa tallace-tallace a titi, domin gudun kar su fada cikin irin wannan mummunan hadari na masu satar yara.
Aminiya ta zanta da yaron da aka sace kuma aka garkame cikin but din motar, mai suna Hassan Musa (dan shekara takwas), wanda ya ce yana tsakar tafiya ne sai mutanen suka bi shi da mota, suka tsaya, suka kama shi da karfi, suka garkama shi cikin but din motar tasu. Kamar yadda ya ce da bakinsa, “Wani kwara ne (Mutumin Lebenon) ya aike ni domin in sawo masa gurasa, shi ne suka tsaya da motarsu, suka ce in zo in amshi sadaka. Bayan na je wurinsu, sai suka kama ni da karfin tsiya, suka kulle ni cikin but din motarsu.”
Shi kuwa shugaban matasan da ake zargi da satar yara, Abubakar Salisu, ya shaida wa Aminiya cewa, ya ga yaran ne suna shakar Sholisho, wanda dalili ke nan ya sanya ya ga ya kamata ya hana su. Ya ce dalili ke nan ya nemi ya tsoratar da su, ta hanyar ladabtar da su domin su daina shan Sholishon. “Dalili ke nan na kama daya daga cikin yaran, na sanya shi cikin but din motar, amma ban rufe but din ba.” Inji Abubakar Salisu.
Ya zuwa yanzu dai, ’yansanda suna ci gaba da binciken al’amarin nan, inda daga bisani za su tura wadanda ake zargi da laifin zuwa kotu.
Al’amuran satar mutane dai na neman zama ruwan dare a Jihar Kano, musamman ganin yadda ake ta samun rahotannin batan yara ko kuma kama wasu da ake zargi da laifin. Idan za a iya tunawa, kwanakin baya ne aka bankado wata maboya a Gundutse da ke karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano, inda ake zargin ana sace mutane, ana kai wa wurin da nufin yin tsafi da sassan jikinsu. Haka kuma, makonni biyu da suka gabata, an kona wani direban tasi har lahira, inda wasu gungun mutane suka yi zargin mai satar yara ne.       
w
 
 

Posted: at 30-03-2010 09:57 PM (14 years ago) | Newbie
- belindajustins at 31-03-2010 08:01 PM (14 years ago)
(f)
no....
Posted: at 31-03-2010 08:01 PM (14 years ago) | Gistmaniac
Reply
- Bazemaster at 31-03-2010 10:02 PM (14 years ago)
(m)
useless

Posted: at 31-03-2010 10:02 PM (14 years ago) | Gistmaniac
Reply
- attamem at 2-04-2010 11:46 PM (14 years ago)
(m)
Malam bahaushe a ringa rubutbn kadan don ba'a aji mukeba.
Posted: at 2-04-2010 11:46 PM (14 years ago) | Upcoming
Reply
- megafather1 at 3-04-2010 12:35 AM (14 years ago)
(m)
tayani gayamishi, irin wannan rubutu ai sai dan hausa.duka yan bura uban basu gane ba
Posted: at 3-04-2010 12:35 AM (14 years ago) | Gistmaniac
Reply
- derbi at 3-04-2010 03:07 PM (14 years ago)
(m)
it sound like one orrable language some people, speak b4 they start killing with dagger and cutlas.
Posted: at 3-04-2010 03:07 PM (14 years ago) | Gistmaniac
Reply
- ibobobelvis at 3-04-2010 04:07 PM (14 years ago)
(m)
no

Posted: at 3-04-2010 04:07 PM (14 years ago) | Gistmaniac
Reply
- Bazemaster at 3-04-2010 11:14 PM (14 years ago)
(m)
Huh??

Posted: at 3-04-2010 11:14 PM (14 years ago) | Gistmaniac
Reply
- onyiis at 10-05-2010 12:49 PM (13 years ago)
(f)
Apears like cultists incantations !!!

Posted: at 10-05-2010 12:49 PM (13 years ago) | Hero
Reply
- iyke1 at 11-05-2010 02:45 PM (13 years ago)
(m)
who no's na him sabi  Lips Sealed
Posted: at 11-05-2010 02:45 PM (13 years ago) | Upcoming
Reply